Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya naɗa Sanata Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin masu magana da yayunsa.

Mutanen biyu za su yi aikin ne a yayin da kakar zaɓen shekarar 2023 ke gabatowa.
Mai bai wa Atiku shawara a kan kafafen yaɗa labarai Paul Ibe ne ya tabbar da hakan a yau Alhamis cikin wata sanarwa da ya watsa.

Sanarwar ta ce mukamin zai fara aiki ne nan take ba tare da ɓata lokaci ba.

Daniel Bwala ɗan jihar Adamawa ya koma jam’iyyar PDP ne daga jam’iyyar APC a makon da ya gabata.
Sanata Dino Melaye tsohon wakili.ne a zauren majalisar dattawan Najeriya kuma ya fito ne daga jihar Kogi.
