Gwamnatin jihar Filato ta soke lasisin makarantu masu zaman kansu a wani yunƙuri na tantance makarantun.

Kwamihsinar ilimi ta jihar Eilizabeth Wampum ce ta tabbatar da hakan yau Alhamis a taron manema labarai.
Kwamishinar ta ce sama da makarantu 5,000 su na aiki ba tare da an basu lasisi a jihar ba.

Sannan kashi 90 cikin 100 na makarantu masu zaman kansu ba su cika ka’idar da gwamnatin jihar ta saka musu ba.

Kuma akwai wasu makarantu da su ke ci gaba da aiki ba tare da sun sabunta lasisinsu ba.
Gwamnatin ta soke lasisin makarantun nazire, firamare, da ƙaramar sakandire da babbar sakandire a jihar har sai ta tantancesu.
A cewar kwamishinar, wannan matakin sun dauka ne domin inganta harkar ilimi daga tushe a jihar.