Rahoton dake fitowa daga karamar hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna, ya nuna cewa yan ta’addan kungiyar Ansaru suna auren matan yankin.

Labarin Angwancewar wasu mambobin kungiyar da matan garin, ya faru ne a garin Tsohuwar Kuyallo a ranar Talata.

Wani dan yankin Birnin Gwari ya tabbatar wa da wakilan BBC cewa irin wannan daurin auren ba sabon abu ba ne a yankin su.

Wani dan yankin ya kara shaidawa BBC cewa, wasu yan mata biyu sun auri mayakan kungiyar Ansaru a watanni biyu da suka gabata.

Rundunar Yan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta ce tana gudanar da bincike akan lamarin.

Wani masanin harkokin tsaro a Jami’ar Ahmadu Bello ABU Zaria, Muhammad Kabir Isa, Ya ce yana ganin sakacin gwamnatin Najeriya a fannin tsaro yasa yan ta’adda ke amfani da irin wannan hanyoyi suna kutsawa cikin al’umma don hada zuria da yan uwantaka na jini da su.

Rashin kulawa da yin abun da ya kamata daga gefen gwamnatin ke sa kungiyoyin yan ta’adda ire-iren su Ansaru suna samun damar janyo mutane a jiki ta hanyar basu tallafi a cewar masani a fannin tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: