Gwanan Jihar Bauchi ya sanya hannu akan wasu dokoki 12 wanda majalisar jihar ta mika masa.

Gwamna Bala Muhammad ya sanya hannu a dokokin ne a jiya Juma’a a far gwamnatin jihar.
Daga cikin dokokin da ya sanyawa hannu ciki harda dokar da za ta tallafawa matasa da kuma kafa kungiyar sa-kai a fadin Jihar.

A yayin jawabinsa gwamna Bala Muhammad ya bayyana cewa gwamnatin ta amince da dokokin ne domin tabbatar da tsaro da kuma taimakawa jami’an tsaron Jihar domin su samu kwarin gwiwar korar bata gari a Jihar.

Bala Muhammad ya kara da cewa daga bisani za a samo hanyar bai wa matasa a Jihar ayyukan yi domin su tallafi rayuwar su.
Sauran dokokin sun hada da samar da hukumar raya burane ta Jihar da kuma samar da hukumar Fansho da kananan hukumomi a shekarar 2022 da mu ke ciki.