Majalisar dokokin Jihar Zamfara ta amince da dokar bayar da kariya ga masu bukata ta Musamman da kuma jindadin al’umar Jihar.

Jami’in yada labarai na Majalisar Nasir Biyabiki shine ya sanya hannu a wasikar hakan tare da rabawa ga manema labarai a Jihar.
A cikin wasikar majalisar ta bukaci a kafa hukumar kula da harkokin masu bukata ta musamma a Jihar Zamfara.

Majalisar ta bayar da umarnin hakan ne bayan da kwamitin kula da harkokin mata da yara kanana na majalisar ya shigar da bukatar hakan inda majalisar ta yi duba akan bukatar tare da amincewa da ita.

Majalisar ta bayyana cewa hakan zai taimakawa gwamnatin Jihar domin ta magance matsalar da masu bukata ta musamman ke fuskanta.
Bayan amince wa da dokar majalisar za ta mika bukatar hakan ga gwamnan Jihar domin ya sanya hannu akan ta.