Wasu ƴan bindiga sun hallaka jami’an ‘yan sanda hudu a lokacin da su ka kai hari wani ofishin yan sanda a jihar Imo.

Lamarin ya farune a daren ranar juma a a garin Agwa da ke cikin karamar hukumar Oguta ta Jihar.
A yayin harin “yan bindigan sun kone wasu motocin ofishin ciki harda ta baturen ƴan sanda wato DPO.

Bayan harin na Ofishin yan sandan yan bindigan sun shiga gidan wani magindanci inda su ka hallaka shi tare da matsar sa.

Wasu majiyoyi daga garin sun bayyana cewa maharan sun shiga garin ne a cikin wasu motoci guda uku.
Sun bayyana cewa zuwan maharan ke da wuya su ka budewa ofishin wuta har ta kai ga sun hallaka jami’an hudu tare da kone ofishin.
Wata majiya daga ofishin yan san ta bayyana cewa an aike da jami’in yan sadan domin su tunkari maharan.
Harin yayi sanadiyyar tayar da hankulan mutanen yanke.
Daga bisani magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya bayyana cewa yan kungiyar IPOB ne su ka kaiwa ofishin hari.
inda ya ce daga cikin mutane hudu da aka hallaka biyu mata ne biyu maza.