Wasu mahara sun hallaka mutane shida a jihar Kogi ciki har da sufurtandan yan sandan
da wasu yan kasar waje biyu a lokacin da su ka kai musu hari.

Yan bindigan sun kai musu harin ne a jiya Juma’a yayin da su ke tafiya.

Kakakin rudunar yan sandan Jihar shine ya tabbatar da lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a garin Lokoja babban birnin jihar a yau Asabar.

Kakakin ya ce mutane an kashe su ne a lokacin da su ka yi musayar wuta da yan bindigan a daren jiya jumaa akan hanyar lokoja zuwa Ajaokuta.

Daga cikin wadanda su ka rasa rayukan su ciki harda dareban yan kasar ta Indiya.

Kakakin ya kara da cewa maharan sun yiwa mutanen kwanton bauna ne a lokacin da su ke yiwa yan kasar waje rakiya zuwa wani kamfani a Ajaokuta a jihar.

Daga bisa an aike da jami’an tsaro wajen don su fatattakesu.

Bayan kai harin kwamishinan yan sanda Jihar ya ziyarci gurin da lamarin ya faru domin ganewa idanunan sa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: