Rahotannin da ke zuwa sun nuna cewa ana zargin wasu ‘Ɓarayi’ sun kutsa gidan gwamnatin jihar Katsina sun yi awon gaba da Miliyan N31m.

Wannan shi ne karo na biyu da aka yi irin wannan aika-aika ta sata a gidan gwamnati, wanda ya kamata ya kasance gini mafi tsaro a faɗin jihar.

A shekarar 2020, An sace makudan kuɗi da suka kai miliyan N16m a ofishin Sakatarem gwamnatin Katsina (SSG).

Manema labarai sun ruwaito cewa a lokacin an kama jami’ai biyu da ke aiki a ofishin Sakataren da wani mai gadi ɗaya da zargin hannu a satar kuɗin.

Wata majiya daga gidan gwamnatin ta shaida wa manema labarai cewa lamarin satar kuɗin ta faru ne tun a ranar 31 ga watan Yuli, 2022.

Majiyar da ta nemi a sakaya bayananta ta ce wasu mutane da ba’a san ko suwaye ba sun kutsa ofishin mai kula da kuɗi na gidan gwamnatin, suka yi gaba da wasu kuɗi a buhu.

Hadimin gwamnan Katsina, Al’Amin Isa, ya tabbatar da sace kudin ga manema labarai amma bai ce komai ba game da adadin kuɗin da aka rasa ba.

Isa ya ƙara da cewa gwamnatin da hukumar yan sanda na kan bincike game da satar kuma babu tantama duk wanda ya aikata zai ɗanɗana kuɗarsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: