Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA reshen jihar Nasarawa ta kama wani da ake zargi tare da kama tan 1,659 na hemp na Indiya wanda kudinsa ya kai N30m.

Da yake gabatar da wanda ake zargin, Kwamandan NDLEA na jihar, Mista Peter Odaudu, ya ce jami’an hukumar ta Akwanga a karamar hukumar Akwanga sun kama direban wani damben J5 me number: KTG 71 XC dauke da hemp din Indiya.

Ya ce direban motar ya taso ne daga Ogere a jihar Ogun zuwa jihar Bauchi.

Ya kuma ce rundunar ta kama 367.6kd na hemp na Indiya tare da kama wasu mutane biyu a kusa da fadar sarkin da ke karamar hukumar Lafia.

Kakakin rundunar yan sanda jihar ta Nasarawa yasanar da cewa zasuyi bincike daga bisani a gurfanar da masu laifi gaban kotu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: