Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta karbe kwangilar aikin jirgin kasa da ta bai wa Kamfanin CCECC mallakin kasar China.
Ministan Sufuri na Najeriya Mu’azu Sambo shi ne ya bayyana hakan a yau Asabar a yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai kan aikin da akeyi a tashar jirgin Ruwa ta APAPA da ke Jihar Legas.
Sambo ya bayyana cewa akwai yuwuwar gwamnatin ta dakatar da kwangilar ne sakamakon rashin mayar da hankali da kamfanin ya yi cikin kaso 85 cikin 100 na kudaden da aka yi yarjejeniya zai bayar dangane da aikin da ake yi.
A yayin jawabin shugaban ya bayyana cewa ya bai wa kamfanin nan da watan Oktoba mai zuwa na shekarar da mu ke ciki da su cika alkawari ko kuma su fuskanci hukunci.
Mininstan ya bayyana cewa shekaru biyu kenan da sanya hannun a yarjejeniyar da aka kulla amma kamfanin na CCECC bai bayar da komai ba.
Mu’azu Sambo ya kara da cewa a cikin yarjejeniyar da su ka kulla da kamfanin zai bayar da kaso 85 cikin 100 na kudin aikin yayin da gwamnatin tarayya za ta bayar da kaso 15 cikin 100 a aikin.