Wasu ‘yan ta’adda da dama sun rasa rayukansu wasu kuma sun samu munanan raunuka bayan da jami’an ‘yan sanda a jihar Katsina suka fatattake su a kauyen Wapa da ke karamar hukumar Kurfi.

A cewar hukumomin ‘yan sanda a jihar, lamarin ya faru ne a daren Juma’a da misalin karfe ɗaya na dare, bayan da aka samu kiran gaggawa cewa ‘yan ta’addan wadanda adadinsu ya kai ashirin da hudu.

Ƴan bindigan sun je a kan babura kuma suna harbe-harbe da bindigogi kirar AK-47, suka far wa kauyen tare da yin garkuwa da mutanen biyu. Aminu Wapa da Wada Sale na kauyen Wapa, karamar hukumar Kurfi.

Bayan samun labarin, rundunar ‘yan sandan jihar ta tura dakarunta a yankin inda suka yi artabu da ‘yan bindigar har da musayar wuta.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu kuma ya fitar a yau Juma’a ya bayyana cewa, tawagar jami’an ‘yan sanda na ci gaba da zage damtse wajen kamo ‘yan ta’addan da suka raunata tare da kwato gawarwakinsu.

Ya ce, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Idrisu Dabban Dauda, ​​ya yaba da kokarin da jami’an suka yi wajen dakile ‘yan ta’addan.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro hadin kai a yakin da suke da ‘yan ta’adda a jihar domin samun nasarar daƙilesu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: