Jami’an tsaron sa kai saama da dubu uku za a bai wa horo a jihar Katsina tare da shirin bazasu sassa daban-daban domin kawo ƙarshen ƴan bindiga.

Mutane 500 daga cikin waɗanda aka bai wa horon sun samu horo ne daga jami’an tsaron ƴan sandan kwantar da tarzoma.
Tuni aka aike da wasu daga cikin jami’an tsaron da aka bai wa horo zuwa ƙananan hukumomin jihar.

mai bai wa gwmana shawara a harkokin tsaro Ahmad Katsina ya tabbtar da hakan a yau Talata.

Ya ce akwai wasu mutane 600 da aka bai wa horo kum ana shirin rarrrabasu zuwa wasu kananan hukumomin jihar.
Ya ƙara da cewa tsarin bai wa mutane horo a kan tsaro za a haɗa kai da sarakunan gargajiya domin samun nasara daga tushe.
Ahmad Katsina ya ce gwamnatin na shirin bayar da horo ga mutabne dubu uku domin ƙarfafa harkar tsaro a jihar ta yadda za a kawo ƙarshen matsalar baki ɗaya.