Rundunar sojin Najeriya ta kori wadanda su ka hallaka Sheikh Goni Aisami akan hanyar sa ta zuwa Jihar Yobe a ranar Juma’a.

Gidan Talabijin na Channels ya rawaito cewa ukaddashin kwamandan Bataliya ta 241 da ke Nguru a Jihar Laftanar Kanal Ibrahim Osabo shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai.

Ya ce sun yanke hukuncin ne bayan da kwamitin binciken da su ka kafa tare da hadin gwiwar jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da mutanen sun aikata laifin kisan.

Ya ce sun kori sojojin ne sakamakon rashin sauke nauyin da aka dora musu tare da sabawa dokokin aiki.

Kanal Ibrahim ya bayyana cewa za su mika sojojin guda biyu ga rundunar ‘yan sandan Jihar da ke Damaturu tare da gurfanar da su a gaban kotu domin yi musu hukunci.

A makon da ya gabata ne wasu sojoji su ka hallaka Goni Ibrahim Aisami bayan ya rage musu hanya da daddare a jihar Yobe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: