Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano hadin gwiwa da Bankin First Bank sun dauki nauyin yiwa mata 150 masu lalurar fitsari tiyata kyauta tare da basu tallafin kananan sana’o’i.

Babban Daraktan hulda da jama’a na bankin First Abdullahi Ibrahim shi ne ya bayyana hakan a lokacin da ya ke kaddamar da shirin.
Daga cikin matan da za a yi musu aiki na yoyon fitsari 50 daga ciki za a yi musu aikin ne a Asibitin Murtala Muhammad da ke Kano.

Sauran 100 kuma bayan an yi musu aikin za a ba su tallafi domin yin kananan sana’o’in dogaro da kai sakamakon wasu daga cikin su su na samun matsalar rabuwa da mazajen su bayan an yi musu aikin.

Tallafin wanda zai gudana karkashin jagoranci First Bank da ke Kano na shirin taimaka wa al’umma domin su dogara da kansu.
A nasa jawabin gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje wanda kwamishiniyar mata da walwalar jama’a Malama Zahra’u Muhammad ta wakilta ya bayyana jindadin sa dangane da kokarin da bankin ya yi na tallafawa matan.