Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa rashin kwarewar Mininstan ilimi Malam Adamu Adamu ne ya sanya Kungiyar ASUU ta ke ci gaba da gudanar da yajin aikin da ta ke yi.

Alhaji Atiku ya bayyana hakan ne a daren jiya Talata a lokacin da ake hira da shi a gidajen rediyoyin Jihar Kano.

A yayin hirar Atiku ya ce gwamnatin tarayyar Najeriya ba ta dauki yajin aikin da kungiyar ta ASUU ke yi da muhimmanci ba wanda hakan ya sanya gwamnatin ta ki kawo karshen yajin aikin da ASUU ke yi.

Alhaji Atiku ya kara da cewa akwai rashin fahimta akan yadda ake tafiyar da tsarin Jami’o’in Najeriya.

Ya ce a lokacin da su ka gana da malam Ibrahim Shekarau wanda ya kasance tsohon Ministan ilimi ya bayyana masa a lokacin da ya na ministan ilimi da ASUU ta shiga yajin aiki ba a yi sati uku ba su ka koma bakin aiki.

Dan takarar ya ce Rashin kwarewar da ministan bashi da ita ne ya sanya har aka kawo yanzu ba a cimma matsaya ba wanda ministan ne ke da alhakin magance yajin aikin.

Atiku ya bayyana cewa duk da kowanne bangare yana da laifi amma gwamnatin ta ki bai wa yajin aikin muhimmanci.

Alhaji Atiku yayi wannan kalaman ne bayan da kungiyar ta ASUU ta ci gaba da yajin aikin da ta ke yi na sai baba ta gani.

Atiku ya ce Jam’iyyar APC ce ta kara jefa Najeriya cikin matsalar rashin tsaro da ake fama da ita da kuma talauci.

Ya ce Jam’iyyar ta APC ba ta yiwa Najeriya wani abin azo a gani ba tare da kin cikawa ‘yan Najeriya alkawarin da ta dauka yayin neman zaɓe.

Leave a Reply

%d bloggers like this: