Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP ya bayyana dalilan da ya sanya Malam Ibrahim Shekarau ya fice daga jam’iyyar.

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da gidan jaridar VOA hausa.

Kwankwaso ya ce Shekarau ya bayyana cewa ba a yi mishi adalci ba a cikin jam’iyyar.

Kwankwason ya kara da cewa kurewar lokaci ne ya sanya ba a bai wa bangaren Malam Shekarau takarar kujeru daban-daban a cikin jam’iyyar ba.

Sanata Kwankwaso ya ce Shekarau bai shigo cikin jam’iyyar ba sai bayan lokaci ya kure.

Kwankwaso ya bayyana cewa sai da aka gama bayar da sunayen ‘yan takara a cikin jam’iyyar sannan Malam Shekarau ya amshi katin shiga cikin jam’iyyar ta NNPP.

Sanatan kwankwaso ya ce a dakko wasu a bai wa kujera ya na da matukar wahala saboda akwai kujerar da mutane 17 su ka nemi su hau kanta.

Kwankwaso ya ce akwai matukar wahala bayan mikawa hukumar zabe INEC sunaye ‘yan takara dan takara ya yarje ya sauka daga kan kujerar.

Ya ce hakan ne ya sanya aka kafa kwamitin da zai kula da bukatun malam Shekarau a cikin jam’iyyar NNPP.

Leave a Reply

%d bloggers like this: