Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya NEMA reshen jihar Borno ta tabbatar da ceto gawarwaki 15 daga wani kogi a jihar.

Shugaban hukumar na shiyyar arewa maso gabashin  Najeriya Muhammad Usman ne ya bayyana haka yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ranar Laraba.

Muhammad Usman ya ce an hakan ya faru ne a sakamakon mamakon ruwan sama da ake samu wanda hakan ya sa rafi da dama ya cika.

Shugaban ya ce ruwan sama wnda ya haifar da ambaliya ya shafi yankuna da dama na jihar.

A sakamakon hakan ne ya sa hukumar ta ja hankalin iyaye da su dinga sa ido a kan ƴaƴansu musamman a yankin arewa maso gabas ganin yadda ake samun ambaliyar ruwan sama a bana.

Sannan hukumar ta fara tunanin samar da hanyoyin wayar da kan jama’a yadda za su kiyaye daga abkwa hatsarin ambaliyar ruwa.

Shugaban ya tabbatar d cewar su na ganawa da masu ruwa da tsaki, da kuma ganawa da waɗanda ambaliyar ya shafa  tare da rage musu raɗaɗin abinda ya samesu.

Daga ɓangaren jami’an tsaro, hukumr kre farren hula ta ƙasa reshen jihar Borno ta aike da jami’anta kududdufi da rafi da kogi domin kare yara daga shiga ciki don tsare rayuwarsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: