Gwamnatin Jihar Kogi ta binne gawarwakin mutane 130 a Jihar wadanda ba a samu ‘yan uwansu ba.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta binne mutanen ne bayan shafe tsawon watanni bakwai a Asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Lokaja.

Gwamnatin ta bayyana cewa mafi yawancin wadanda aka binne su hadarin mota ne da kuma wadanda ‘yan ta’adda su ka hallaka.

Mutanen da gwamnatin ta Jihar ta Kogi ta binne ta binne su a makabartar Felele da ke garin na Lokoja.

Shugaba a hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta Jihar Elizabath Arokoyo ta bayyana cewa doka ta bai wa hukumar share dukkan wane guri da ke fadin Jihar.

Shugabar ta ce sun dauke matakin binne mutanen ne sakamakon dadewar da mutanen su ka yi a cikin Asibitin ba tare da wasu ‘yan uwan su sun zo daukar su ba.

Elizabath ta kara da cewa sun dade su na bayar da sanarwa a kafafen yada labarai amma ba a samu ‘yan uwan mutanen ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: