Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta ce ta soke rijistar katin zaɓe na mutane 1,126,359 a Najeriya.

Kwamishinan zaɓe a Najeriya Fetus Okoye ne ya sanar da haka a sanarwar da hukumar ta fitar mai ɗauke da sa hannunsa.
Hukumar ta ce ta soke rijistar mutanen ne domin ba su yi rijistar yadda ya kamata kamar yadda doka ta tsara ba.

Hukumar ta ce akwai mutane 1,397,099 da su ka yi sabuwar rijistar katin zaɓe kuma su kaɗai ne za su yi zaɓe tare da sakasu a cikin adadin mutanen da su ke da katin zaɓe halastacce kuma ingatacce a Najeriya.

A binciken da hukumar ta yi ta gano cewar, akwai mutanen da su ka yi rijistar katin zaben sai biyu wasu ma fiye da biyu kuma hakan ta sanya aka soke rijistarsu.
Hukumar ta tabbatar da cewar katin zaɓen da mutane su ka yi zai kammala tare da fara rabawa daga karshen watan Oktoba da kuma farkon watan Nuwamba.
