Wata babbar kotu da ke garin Damaturu babban birnin Jihar Yobe ta fara sauraron karar wadanda su ka hallaka Sheikh Goni Aisami a Jihar.

Alkaliyar Kotu Amina Shehu ta dage sauraron shari’ar da aka fara yau bayan bangaren gwamnatin sun nemi da a sake dage sauraron shari’ar.

Alƙalin alƙalai na Jihar Brisster Saleh Samanja ne ya roki kotun da ta bai wa tawagarsa ta masu gabatar da kara wadataccen lokaci su hada shaidu domin gudanar da shari’ar yadda ya kamata.

Bayan rokon da alƙalin alƙalai na Jihar yayi Alkaliyar kotun ta dage sauraron shari’ar inda ta bayyana cewa za a sanar da kowanne bangare ranar da za a ci gaba da gudanar da shari’a.

Idan ba a manta ba a watan Augustan da ya gabata ne wasu jami’an tsaron soji biyu su ka hallaka Sheikh Goni Aisami a lokacin da ya ke kan hanyar sa ta zuwa Jihar Yobe.

Bayan faruwar lamarin rundunar sojin tsaro ta Najeriya ta kori jami’an daga bakin aiki tare da mikasu ga hannun jami’an yan sanda domin gabatar da bincike tare da gurfanar da su a gaban kotu don yi musu hukunci akan abinda su ka aikata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: