Hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa SEMA reshen jihar Kano ta ce akalla gonaki 14,496 Ambaliyar ruwa ta yi sanadin lalacewar su cikin kananan hukumomi biyar na Jihar Kano.

Babban daraktan hukumar Mustapha Ahmad Habib ne ya bayyana hakan ga manema labarai jiya Talata.
Daraktan na wannan jawabin a yayin wani zagayan tantancewa da ya kai wa mutanen kananan hukumomin warawa da Wudil da ke Kano wanda Ambaliyar ruwa ta shafa.

Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa shugaban ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammad Buhari ya bai wa hukumar izinin kididdige ɓarnar da ambaliyar ruwan ta yi tare da alkawarin bai wa wadanda ambaiyar ruwan ta shafa tallafin wasu kayayyaki domin rage musu radadin halin da su ke ciki.

Mustapha Ahmad ya ce daga cikin kananan hukumomin da abin ya shafa sun hada da ƙaramar hukumar Bebeji, Rano, Warawa, Wudil, da kuma dawakin Kudu.
Daraktan ya kara da cewa a garin Bebeji gonaki 1,405 ne su ka lalace sai Rano 260 yayin da karamar hukumar dawakin Kudu kuma gonaki 5,775 su ma su ka lalace.
Sauran sun hada da gonakin garin Wudil 4,808 a Warawa kuma gonaki da ke gishirin wuya gonaki 1,113 sai Larabar gadon Sarki gonaki 1,135 dukkan ambaliyar ruwan ta yi awon gaba da su.
Darakan ya ce sakamakon yanayin hanya a wasu yankuna da abin ya shafa a karamar hukumar Warawa ba su samu damar shiga gonakin ba saboda tsoron makalewar da motocin su ka yi.
Ahmad Habib ya kara da cewa bayan makalewar motocin su ka nufi wasu yankuna da ke garin Wudil.
Daraktan ya ce bayan kammala rahoton tantancewar za su mikashi ga ma’aikatar jin kai da kula da ibtilati da kuma ci gaban jama’a domin aike wa da shi ga shugaban kasa Muhammad Buhari.
Mustapha Ahmad Habib ya bayyana cewa a lokaci da hukumar su za ta samar da kayan tallafi ga wadanda abin ya shafa gwamnatin tarraya za ta za ta sanya hannu cikin gaggawa domin bai wa manoman tallafi ta yadda za su iya dawo da asarar da su ka tafka.