Hukumar kare fararen hula a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wani matashi mai shekara 10 a duniya.

Matashin ya mutu yayin da ya je yin wanka wani kogi a ƙauyen Lelen Kudu shi da abokansa.

Mai magana da yawun hukumar NSCDC reshen jihar Jigawa Adamu Shehu ne ya tabbatar da haman yayin ganawa da kamfanin dillancin labarai a Najefiya NAN.

Matashin sun je wanka shi da abokansa ne ranar Asabar a ƙaramar hukumar Buji ta jihar Jigawa.

Ya ce awanni biyu bayan cetoshi likita a jihar ya tabbatar da mutuwarsa.

Idan ba a manta ba, a kwanakin baya aka aike da jami’an hukumar kare fararen hula ta Civil Defence kogu da rafi da kuddudufi na Jigawa domin hana yara da matasa shiga yin wanka tun bayan da aka fara ambaliyar ruwan sama a daminar bana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: