Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce babu jihar da ta ke da ikon bai wa ƴan jihar izinin riƙe makami.

Bayanin hakan wanda mai magana da yawun shugaban ƙasa Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce babu jihar da ta ke da lasisin bayar da izinin riƙe makami ga ɗaiɗaiku ko wata hukuma a jihar.

Hakan martani ne ga gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredelu wanda ya ce ba zai ja da baya ba wajen bai wa jami’an Amoetekun izinin riƙe makami domin aikin tsaro a jihar.

A ranar Litinin gwamnan ya jaddada hakan a yayin da ya ke bayyana irin ayyukan sabuwar hukumar tsaro a jihar.

Tun a baya gwamnonin jihohin kudancin Najeriya su ka nuna sha’awar kafa jami’an tsaron jihohi domin samar da tsaro.

Sai dai gwamnatin tarayya ta yi martani da cewar babu wata jiha da aka ba ta izinin da za ta kafa jami’an tsaro har su riƙe makami.

Sannan gwambatin ta ce duk wanda ya riƙe makami wajibi ne ya miƙa kansa ga jami’an tsaro.

Malam Garba Shehu ya bayar da misali da jihar Katsina, ya ce gwamnan ya rubuta takarda ne domin neman izinin jami’an hukumar kare fararen hula ta yadda za su bai wa ƴan sa kai horo domin taimakawa tsaro.

Ya ce hakan ba ya na nufin su maye gurbin jami’an ba illa su taimaka musu a ayyukansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: