Gwamnatin Tarayya ta ja kunnen Kungiyar Malaman Jami’a akan ƙin bin dokar Kotun Ma’aikatun Kasa ta Najeriya na komawa bakin aikinta daga dogon yajin aikin da ta ke yi.

Chris Ngige, Ministan Kwadago da Ayyuka, ya ce Kungiyar tana faɗawa ‘yan Najeriya zancen da babu sui akan batun cikashe fom din daukaka karar akan umarnin kotu.
Ministan ya yi kira ga kungiyar akan ta mutunta umarnin kotun, ta kuma koma kan aikinta yayin da su ke kokarin ganin sun sasanta akan sauran matsalolin.

Ministan ya yi wannan batun ne ta wata takarda da aka fitar a ranar Lahadi wadda Olajide Oshundun, mataimakin darektan yaɗa labaran ministan ya sanyawa hannu.

A cewar sa kungiyar ba ta fadin asalin gaskiyar yadda aka yi da ita ga mutanen ƙasa da kuma mambobinta, dangane da batun daukaka kara bisa umarnin da kotu ta yi mata ranar 2 ga watan Satumba.
Sai dai ASUU ta bukaci a ba ta damar daukaka kara. Sannan ta hada wannan bukatar tata da kuma takardar daukaka karar da ta ke da niyar yi da zarar an bata wannan damar.