Akalla mutane 41 ne suka kamu da cutar Kyandar biri cikin kwanaki Bakwai a fadin Najeriya.

Hukumar dake dakile cututtuka masu yaduwa NCDC itace ta bayyyana haka a shaifin ta a ranar Lahadi cikin sakon da ta saba fitarwa a Twitter.
NCDC ta ce mutane 41 ne suka kamu da annobar cutar Kyandar biri daga ranar 29 ga watan Augusta zuwa 4 ga watan satumba shekarar da muke ciki.

Sannan cikin jihohin da masu annobar suka fito mafi yawanci daga kudancin kasar ne kuma sun hada da Jihar Legas da 14 sai Abia 7 da kuma Imo 6 Ogun 5 Ondo 2.
Sauran jihohin su ne Akwa Ibom 1 Borno 1 Delta 1 Oyo 1 Plateau 1 Rivers ma mutum 1.

Sannan mutane dake dauke da cutar a halin yanzu sun kai su 318 bayan mutuwar mutane 7 a fadin Najeriya.
NCDC ta ci gaba da bayyyana cewa cutar Kyandar biri cuta ce wadda ke zuwa lokaci ta na kara yaduwa a kasashen Afrika musamman ga yankin talakawa.
Sannan Kyandar biri ta hallaka mutane da dama kuma ta fi tasiri akan yara kanana.
Kuma hukumar na ci gaba da dakile cutur a fadin kasar ta yadda za a kawo karshen matsalar a fadin baki ɗaya.