Iyalan shaharraren malamin adinin nan da aka yiwa kisan gilla wato Shiek goni Aisami dan asalin jihar Yobe sun bayyana cewa sun damu matuka akan yadda har yanzu ba su ji an hukunta sojan da ya hallaka mahaifin nasu ba.

Daya daga cikin iyalan malamin mai suna Abdullahi Goni Aisami ya bayyana cewa ba su ga dalilin da zai haifar da tsaiko a cikin lamarin ba.

ya ce sun shiga fargaba da tashin hankali saboda kin samun wata hujja akan kin gurfanar da sojin a gaban kotu.

ya ci gaba da cewa suna cikin matsalar musamman daga bangaren matan malamin da su ke gani kamar ba wani hukunci akai ba.

Sai dai a bangaren hukuma kakakin rundunar yan sandan jihar Yobe DSP Dungus ya bayyana cewa tun lokacin da su ka kammala bincike suka turawa hukumar shariar domin gurfanar da wadannan sojoji guda biyu a gaban kotu.

Sannan ya ce an yi nasarar yin hakan a ranar 19 ga wata Satumba aka zauna domin sauraren shari’ar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: