Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta sanar da cewar za ta yi aiki da jami’an tsaro na sirri domin daƙile siyan ƙuri’a a lokacin zaɓe.

Hukumar ta sha alwashin daƙile aikin siyen ƙuri’u kafin zaɓen shekarar 2023 mai gabatowa.
Kwamishinan zaɓe na ƙasa kuma shugaban kwamitin wayar da kai jama’a a kan katin zaɓe Festus Okoye ne ya sanar da hakan.

Ya sake nanata aniyar hukumar na tabbatar da adalci a zaɓen shekarar 2023.

Sannan ya ce za su yi aiki da jami’an tsaro don ganin an daƙile duk wata hanya ta maguɗin zaɓe musamman siyar da ƙuri’a.
Hukumar ta ce za ta yi amfani da jami’an tsaron ne cikin sirri kuma a ranar zabe domin daƙile batun siyar da ƙuri’a.
Tun a baya hukumar ta sha nanata cewar ta magance dukkan wata hanya ta maguɗin zaɓe illa siyan ƙuri’a wanda hakan ke yi wa hukumar barazana, sai dai a wannan lokaci ta samo mafita domin daƙile hakan.