Shugaban majalisar wakilai a Najeriya Femi Gbajabiamila ya yi wata ganawa da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari domin ganin an shawo kan yajin aikin malaman jami’a.

Femi Gbajabiamila ya jagoranci tawagar wasu daga cikin ƴan majalisar wakilai don ganawa da shugaban ƙasa yadda za a shawo kan yajin aikin.

A yayin ganawar da su ka yi da shugaban ƙasa, sun gabatar da wasu shawarwari da su ke ganin za su kawo ƙarshen yajin aikin da aka shafe watanni ana yi.

Shugaban majalisar ya ce za su kuma ganawa ta ƙarshe da shugaba Buhari a gobe Alhamis, kuma a yayin ganawar za su ɗauki mataki na ƙarshe a dangane da yajin aikin.

Sannan ya sake tabbatar da cewar nan ba da jimawa ba za a kawo ƙarshen yajin aikin da malaman su ka shafe wtanni takwas su na yi.

Tun a baya majalisar wakilai ta nuna amuwarta a dangane da yajin aikin malaman jami’a ASUU su ke yi domin jan hankalin gwamnati na ganin ta cika musu buƙatunsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: