Gwamnatin tarayyar Najeriya ta musanta batun da ake zargi na siyar da kamfanin rarraba wutar lantarki na ƙasa TCN.

Ma’aikatar rarraba wutar lantarki ta ƙasa TCN ce ta musanta batun a wata sanarwar da ta fitar yau Laraba.
Ta ce gwamnati ba ta da shirin siyar da kamfanin domin mayar da shi hannun wasu tsirarun mutane a ƙasar.

A yan kwanakin nan labari ya karaɗe kafofin sada zumunta cewar, gwamnatin na shirin siyar da kamfanin rarraba wutar nan da watanni kaɗan masu zuwa.

Kamfanin ya musanta batun tare da bukatar yan kasar da su yi watsi da jita-jitar.
A cewar kamfanin TCN, gwamnatin shugaba Buhari ta mayar da hankali a kan yadda za ta bunƙasa kamfanin ta yadda ƴan ƙasa za su ci gaba da samun wutar lantarki ba tare da wata matsala ba.
Tuni gwamnatin ta haɗa kai da ɓangarori masu zaman kansu da ma kasashen ketare don ganin an farfaɗo da kamfanin tare da dakile ƙalubalen da kamfanin ke fusknata.