An ci gaba da samun mutuwar mutane a jamhuriyar Nijar sakamakon ambaliyar ruwan sama a bana.

Rahotanni sun nuna cewar mutanen da su ka mutu sun kai 195 yayin da ambaliyar ta shafi mutane 322,000.

 

Hukumar bayar da kariya ga jama’a ta Civil Protection, Services APS ta tabbatar da cewar fiye da gidaje 30,000 sun lalace a sanadin ambaliyar ruwan.

Sannan an cibiyar lafiya guda shida da kuma manyan ɗakunan ajiya guda 235.

Hukumar ta ce wuraren da ambaliyar ruwan ta fi shafa su ne Zinder, Maraɗi, Dosso da kuma Tahoua.

Hukumar kula da yanayi ta ƙasar ta ce ambaliyar ruwan ta samo asali ne a sanadin sauyin yanyi da aka samu a bana.

Ko a Najeriya ma, akwai jihohi da dama da ambaliyar ruwan saman ya shafa wanda hakan ya yi silar rasa rayuwar wasu mutane.

Leave a Reply

%d bloggers like this: