Ma’aikatar jin ƙai da rage raɗaɗi a Najeriya ta tabbatar da cewar a daminar bana mutane sama da 600 ambaliyar ruwa ta yi sandiyyar mutuwarsu.

Ministar jin ƙai a Najeriya Hajiya Sadiya Umar Fatuƙ ce ta bayyana haka bayan da hukumar ta gudanar da wata kididdiga a kan ibtila’in ambaliyar ruwan a bana.
Ƙididdigar da su ka yi ta nuna cewar gidaje 8,053 ne su ka rushe kuma hakan ya shafi mutane 1,302,589.

Sai kuma mutane 2,407 da su ka samu munanan rauni a sanadin ambaliyar ruwan sama a bana.

Ministar ta ƙara da cewa har yanzu ba a fita daga fargabar sake fuskantar ambaliyar ruwan ba, domin akwai jihohin da ka iya fuskantar ambaliyar ruwan a nan gaba.
Jihohin da aka ambata su ne Anambra, Rivers, Bayelsa, Cross River, da jihar Delta.
Ministar ta ce ambaliyar ruwan da aka fuskanta a bana ta sa ma’aikatar gudanar da ayyuka masu yawan gaske domin ganin an rage raɗaɗi ga mutanen da ya shafa.