Hukumomi a babban birnin tarayya Abuja sun bayar da umarnin sanya kyamarorin tsaro a wuraren taruwar jama’a.

Hakan ya biyo bayan wani bayanai da su ka baxu cewar wasu mahara na shirin kai hare-hare babban birnin tarayya Abuja.
An cimma matsayar sanya kyamarorin tsato ba tare da ɓata lokaci ba a dukkanin wuraren taruwar jama’a da ke Abuja.

Guda cikin mahukunta a tsakiyar binrin tarayya Abuja Umar Shu’aibu ya shaida hakan bayan wani taro da aka cimma matsayar hakan ranar Alhamis makon jiya.

Ya ce gwamnatin na duba halin da ake ciki na tsaro hakan ya sa su ke shirya tsaro don tattauna matsalolin tsaro da kuma yadda za a kare rayuwa da dukiyoyin al’umma.
An ƙara tsaurara matakan tsaro a Abuja bayan da wasu bayanai daga ofishin jakadancin amuruka ya fita cewar wasu mahara na yunƙurin kai hare-hare wuraren taruwar jama’a a babban birnin tarayya Abuja a Najeriya.
