Ƙungiyar likitici a Najeriya reshen jihar Nassarawa ta tabbatar da cewar fiye da ma’aikatan lafiya 100 ne su ka bar aiki tare da tsallakawa ƙasashen ketare.

Shugaban ƙungiyar Dakta Peter Attah ne ya bayyana haka yau a Lafiya babban birnin jihar.
Ya ce akwai kwararrun likitoci da su ka tafi daga asibitin gwamnatin tarayya a jihar da asibitin koyarwa na jihar kuma hukumar lafiya ta jihar.

Ya kara da cewa likitocin sun tafi zuwa ƙasar saudiyya domin cigaba da gudanar da ayyukansu a can.

A cewar shugaban, likitoci 100 da su ka bar jihar zuwa ƙasar Saudiyya sun tafi ne cikin ahekara guda.
Sai dai ya alaƙanta hakan da rashin kyakkyawar kulawa da likitocin ba sa samu daga mahukunta.
A cewarsa a jihar kowanne likita na duba marasa lafiya 20,000 saɓanin 10,000 da ake dubawa a sauran jihohin Najeriya.