Rundunar yan sanda a jihar Sokoto sun kama wani mai suna Nasiru Idtis ɗauke da katin zaɓe guda 101.

Kwamishinan ƴan sanda a jihar Hussain Gumel ne ya sanar da haka a yayin ganawa da manema labarai yau.

Ya ce an kama mutumin a ƙaramar hukumar Sabon Birni a ranar 10 ga watan Oktoban shekarar da mu ke ciki.

Kwamishinan ya ce sun samu bayanai a kan wanda ake zargi wanda hakan ya yi sanadin kamashi.

Sai dai ya ce katin zaben na mutane daban-daban ne da ke sassan jihar.

Hakan ya sa hukumar ke buƙatar wand akatinsa ya ɓata domin ya hanzarta zuwa ko zai samu nasa a ciki.

Ya ce bayan wata guda, hukumar yan sanda za ta mayar da katin zaɓen ga hukumar zaɓe mai zaman kanta reshen jihar.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: