Yayin da ake barazanar harin yan ta’addan a birnin tarayya Abuja, Gwamnatin Amurka ta bukaci iyalan ma’akatansu dake zama a Abuja su bar birnin da gaggawa.

Wannan na kunshe cikin sabon ummarni da ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya ya fitar a yau Juma’a.

Hakan ya biyo bayan jawabin Amurka na cewa shirye take da ta fara kwashe yan kasarta dake Najeriya.

Tuni aka rufe babban kantin Jabi Lake Mall dake unguwar Utako a birnin tarayya Abuja ta rufe dukkan shagunanta ranar Alhamis sakamakon barazanar tsaron da ake yiwa garin.

A jawabin da kantin ya ɗora a shafinsa na Instagram hukumomin sun bayyana cewa duk da cewa ba tada niyyar tadawa mutane hankali, sun yanke shawarar haka ne domin kare rayukan masu zuwa siyayya da ma’aikatanta.

Sun kara da cewa suna bibiyar yadda al’amarin ke gudana kuma idan komai ya daidaita za’a bude a nan gaba

Leave a Reply

%d bloggers like this: