Rahotanni daga Jihar Zamfara sun bayyana cewa wasu ‘yan Bindiga sun yi garkwa da basaraken kauyan Birnin Tsaba da dan uwansa da ke karamar hukumar Zurmi ta Jihar.

Wani mazainin garin mai suna Muhammad Faruku ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Punch ya ce ‘yan bindigan sun yi garkuwa da mutanen ne da Asubahin yau Asabar.
Faruku ya kara da cewa ‘yan bindigan sun zo ne akan babura da misalin karfe 3:00 zuwa 4:00 daga bisani kuma bayan shigar su gidan garin su ka yi garkuwa dashi da dan uwansa.

Shima wani daga cikin dan uwan mai garin ya bayyana cewa wani shahararran dan bindiga da ke yankin ne ya daukin dauyin aikata ta’addancin.

Ya ce sakamakon dauke wa ‘yan bindigan babur guda biyu da jami’an tsaro su ka yi ne su ka dauki matakin hakan.
Ya kara da cewa kawo yanzu ‘yan bindigan sun nemi kudin fansa domin sakin mutanen.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar bai ce komai ba akan lamarin.