Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen jihar Kaduna, ta ce, ta kwace kayayyaki daban-daban har 132 da akayi fasakwaurin su da darajar kudinsu ya kai Naira N690,821,657.94 a cikin kwanaki 60 da suka gabata.

Shugaban hukumar da ke kula da shiyyar Kaduna da sauran maƙobta Albashir Hamisu wanda ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai jim kadan bayan baje kolin kayayyakin da aka kwace daga jihohin yankin.

Shugaban ya yabawa rundunar sojin Najeriya bisa gudunmawar da suka ba su wajen samun nasarar bankado masu fasa-kwaurin.

Ya ce, duk da cewa masu fasa-kwaurin suna amfani da kwarewa, amma duk da haka, hukumar kwastam ta kan iya gano su, kuma za ta ci gaba da kwace kayayyakin su har sai sun daina yi wa Tattalin Arzikin kasa zagon kasa.

Kayayyakin da aka kama sun hada da dilar kayan gwanjo 758 da buhunan shinkafa 749 ta kasar waje da wasu ƙananan buhunan shinkafar kasar waje 65 da katan 533 na taliyar kasashen waje da macaroni da kuma katon 473 na kayayyakin magunguna na kasashen waje.

Sauran kayayyakin sun hada da fakiti 70 na tabar wiwi da jarka 59 na man gyada da buhuna 47 na takin kasashen waje.

Sannan sun kama gwanjon tayoyin mota 245 da jarkar man fetur 221 (25lita) ) da katan 116 na takalman mata na kasashen waje da jarkar man gyada 10.

Haka kuma, an baje kolin motoci guda 24 da suka hada da guda 4 da aka yi amfani da su wajen jigilar kayayyakin da kuma motocin hawa 20 da katan 14 na man gyaran jiki na kasashen waje da katan 12 na tabar sigari da buhu 39 na gwanjon takalma da buhu biyu na gwanjon jakunkuna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: