Anyi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara wa’adin da ta diba kafin sauya fasalin kudin kasar.

Wata kungiya mai suna Arewa Youth’s Awareness and Social Development, tayi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya da ta kara wa’adain da ta diba kafin sauya fasalin kudin kasar.

Kungiyar ta bakin kakakinta na kasa Muhammad Chigari Kumo, ta bayyana cewa rashin kara wa’adin ka iya kawo nakasu ga tattalin arzikin kasar, Chigari kuma ya bayyana cewa a halin da kasar ke ciki akwai bukatar ace gwamnati ta bada wada taccen lokaci, duba da al’umma mazauna karkara da basu da wayewar yin alaka da bankuna wajen ganin basu yi asara ba.

A ganawarsa da wakilinmu, mai magana da yawun kungiyar Chigari Kumo yace a halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu babu bukatar sauya fasalin kudin kasar, yace idan aka kwatanta darajar Naira zuwa Dallar Amurka kyautuwa yayi gwamnati ta samo hanyoyin tattalin arziki da zasu daga darajar Naira ba maganar sauya fasalin kudin kasar ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: