Gwamnan jihar Edo Godwin Obaseki ya sauke kwamishinan tituna da gadoji na jihar Injiniya Newton Okojie daga kan kujerarsa.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Mr.
Chris Osa, da aka bara ga manema labarai. Sanarwa tace gwamna Obasake ya dauki wannan matakine biyo bayan kasa gudanar da aiki yanda ya kamata daga kwamishinan.

Sanarwa ta kara da cewa gwamnan ya godewa kwamishinan bisa kokarisa na shidimtawa al’ummar jihar.

Gwamnan ya kuma umarci babban sakatare na ma’aikatar Injiniya Osikhena Omoh Ojior daya rike ma’aikatar kafin nadin sabon kwamishinan da zai maye gurbin Injiniya Newton Okojie.