Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya amince da nadin sabbin kwamishinoni tara a jihar.

A wata sannarwa mai dauke da sa hannun sakataran gwamnatin jihar Kebbi Babale Umar Yauri, da aka raba ga manema labarai a Birnin Kebbi, tace gwamna Bagudu ya amince da nadin Abubakar Chika Ladan a matsayin kwamishinan ayyuka da sufuri, kana gwamnan ya amince da nadin Abdullahi Muhammad Magoro a matsayin kwamishinan yada labarai da al’adu, wanda kuma zai lura da ma’aikatar Sadarwa ta jihar.
Sauran wadanda aka nada sune Hassan Muhammad Shalla ma’aikatar ilmi matakin farko, sai Aminu Garba Dangida a matsayin kwamishina mai kula da lafiyar dabbobi.

Sabbin kwamishinonin sun hada da Dr. Abba Sani Kalgo a matsayin kwamishinan kasafi da tattalin arziki, sai Ja’afar Muhammad ma’aikatar lafiya, sai Mamuda M wara a matsayin kwamishinan ma’aikatar kasa da gidaje, kana gwamnan ya amince da nadin Hayatu A. Bawa a matsayin kwamishinan muhalli na jihar.

Sanarwa tace nadin ya fara aikine nan take.