Jami’ar gwamnatin tayyya dake Dutse ta kayyade maki 150 a matsayin maki mafi karanci na shekarar karatu ta 2022 zuwa 2023.

Jami’ar ta sanar da maki 150 a matsayin mafi karanci na samin gurbin karatu na wannan shekara, ga dabiban da suka sanya jami’ar a za6in farko.

FUD ta kuma sanar da cewa daga ranar litinin 31 ga watan oktoba zuwa ranar 4 ga Nuwamba zatayi aikin tantance wadanda ke neman gurbin karatu a jami’ar ta hanyar JAMB, DE, da kuma IJMB.

A sanarwar da kakakin jami’ar Abdullahi Bello ya fitar, yace jami’ar na shawartar dalibai dake neman gurbin karatu na shekarar 2021 da suyi maza su kammala tantancewa kafin ranar 4 ga watan Nuwamba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: