Akalla mutane 17 ne su ka rasa rayukan su a lokacin da wasu ‘yan bindiga su ka kai musu hari a karamar hukumar Guma da ke Jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta rawaito ce mai bai wa shugaban karamar hukumar shawara kan sha’anin tsaro Chistopher Waku ne ya tabbatar da kai harin.
Waku ya ce Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 5:00 na yammacin ranar Alhamis a lokacin da al’ummar su ke tsaka da hada-hadar kasuwanci yankin.

Shugaban ya kara da cewa kawo yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano wadanda su ka bace.

A yayin tabbatar wa da manema labarai lamarin shugaban karamar hukumar Mike Ubah ya ce ‘yan bindigan sun isa gurin ne sanye da bakaken kaya inda kuma zuwan su ke da wuya su ka budewa mutanen kasuwar wuta tare da hallaka mutane goma.
Shugaban na karamar hukumar ta Ubah ya ce baya ga harin kasuwar sun kuma koma wasu kauyukan da ke kusa da yankin su ka hallaka mutane Bakwai.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Cathrine Anene ta tabbatar da faruwal lamarin.