Gwamnatin jihar Kano ta karyata rahotannin cewa Gwamna Abdullahi Ganduje na cikin jerin gwamnoni uku da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta zuba idanu a kansu kan cewa sun boye kudade a gidajensu.

Jaridar Punch ta rahoto cewa gwamnati ta yi martani ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, ya fitar a ranar Lahadi, 6 ga watan Nuwamba.

Kwamishinan ya bayyana cewa yayin da EFCC bata ambaci sunayen gwamnonin ba, jaridar yanar gizon ta yi gaban kanta wajen yin wannan kagen.

Ya ce mawallafin rahoton wanda baida tushe balle makama hasashe yana hasashe ne kawai ko kuma dai an kagi labarin ne don bata sunan gwamnan.

Garba ya bayyana cewa Gwamna Ganduje bai mallaki biliyoyin nairori sannan ya yi ruf da ciki a kansu ba.

Kwamishinan ya kara da cewa Kano na daya daga cikin yan tsirarun jihohi da ke biyan albashin ma’aikatanta a kan kari, yana mai cewa a daidai lokacin da aka saki rahoton karyan, an rigada an fara tura albashin watan Oktoba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: