Tsohon shugaban Amurka Donal Trump, yace dole ne su kwace muulkin kasar daga wadanda ke jagorantarta a halin yanzu.
Trump yace al’ummar kasar su tsumayi sanarwa ta musamman da zai fitar ranar ga watan Nuwamba.

Ya ce zai bayyana sanarwar tasa ne a gabar tekun shakatawar Maralago da ke Florida.
Tsohon shugaban ya ce jam’iyarsu ta Republican a shirye take ta kwace majalisar kasar a zabukan da za’a gudanar, yana mai cewa zasu kwace majalisu, dama kasar baki daya.

kuma a shekarar 2024 za su sake shiga fadar mulki ta white house a cewarsa.
Trump na wannan jawabine kwana guda gabanin zaben ‘yan majalisar wakilai da na Dattawa da kuma yanke mahimman shawarwari kan kujerun gwmnoni da sauran mukamai.

Kalaman na Trump sun haifar da jita-jitar cewa zai sake tsayawa takara a 2024, duk da bai fito karara ya bayyana hakanba ko a hukumance.