Connect with us

Labarai

Ƴan Sanda Sun Kama Mutanen Da Su Ka Yi Garkuwa Da Wata Alƙaliya A Kwara

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da wata babbar alkaliya kotun majistire a jihar mai suna Misis Jumoke Bamigboye.

A ranar Asabar ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Jumoke Bamigboye, wadde ta kasance matar tsohon shugaban mulkin soja na jihohin Bauchi da Osun, inda suka saketa a daren Litinin bayan kwashe kwanaki uku a hannunsu.

An sace matar ne a unguwar Oko-Olowo da ke Ilorin, babban birnin jihar, yayin da take dawowa daga gonarta.

Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun bukaci a biya su Naira miliyan 100 domin su sako ta amma daga baya su ka yanke kudin zuwa Naira miliyan 50 bayan tattaunawa da iyalanta.

Duk da cewa mijin nata, Kanal Theophilus Bamigboye (mai ritaya), ya tabbatar da cewa an biya kudin fansa ga masu garkuwa da mutanen, bai bayyana takamaiman adadin kudin da aka biya na sakin ta ba.

Theophilus dai ya ce an kai ta asibiti domin kula da lafiyarta bayan an sako ta daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Kakakin rundunar ‘yansandan Jihar Kwara, Okasanmi Ajayi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Talata a Ilorin, ya bayyana cewa an kama wasu mutane uku da ake zargi da yin garkuwa da ita yayin da ake ci gaba da neman  sauran wadanda ake zargi da hannu a ciki.

Click to comment

Leave a Reply

Labarai

Mai Maganin Gargajiya Ya Harbi Kansa Bayan Yin Gajin Maganin Bindiga

Published

on

Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya harbi kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindiga a yankin Kuchibiyi da ke Karamar Hukumar Bwari a birnin Abuja.

Wani mazaunin Kuchibiyi Samson Ayuba ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, a lokacin da mutumin ya ke kokarin gada ingancin maganin bindgar da ya hada.

Ya ce sai dai bayan faruwar lamarin an yi gaggawar kai shi asibitin gwamnati da ke Kubwa bayan ya fadi, inda kuma ya samu raunuka.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja Joesephine Adeh ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ta fitar.

Adeh ta ce sun samu rahotan cewa wani mai maganin gargajiya ya harbe kansa a lokacin da yake gwajin maganin bindigar da ya hada.

Sai dai ta ce sakamakon munanan raunukan da ya samu aka kai shi asibitin Kubwa domin duba lafiyarsa, daga bisani kuma aka mayar da shi asibitin kwararru da ke Gwagwalada domin kara samun kulawa.

Kakakin ta kara da cewa abinciken da aka gudanar a gidansa an gano wata bindigar gargajiya da layu wadanda ya yi amfani da su gurin gwajin maganin bindigar.

Adeh ta ce a halin yanzu su na ci gaba da gudanar da bincike kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu bisa zarginsa da mallakar makami ba bisa ka’ida ba tare da yunkurin hallaka kansa.

 

Continue Reading

Labarai

Jami’an Soji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda Sama Da 100 A Sassan Najeriya A Mako Guda

Published

on

Rundunar sojin Najeriya ta ce jami’anta sun samu nasarar hallaka ‘yan ta’adda 135, tare da kama mutane 185 da ake zargi da aikata laifuka, da kuma ceto mutane 129 da aka yi garkuwa da su a sassa daban-daban na fadin Kasar nan a cikin mako guda.

Daraktan yada yada labaran hedkwatar tsaro ta Kasa Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan ne a yau Asabar a hedkwatar da ke Abuja.

Buba ya ce daga cikin wadanda aka kama ciki harda 61 da ake zargi da satar mai.

Acewar Buba ‘yan ta’adda a yankin Arewa ta tsakiya sun fara mika wuya ga sojojin su.

Continue Reading

Labarai

Gwamnatin Kano Ta Mayarwa Da Jami’ar Yusuf Maitama Sule Asalin Sunanta

Published

on

Gwamnatin Jihar Kano ta mayarwa da Jami’ar Yusuf Maitama Sule tsohon sunanta na asali.

Majalisar Zartarwar jihar ce ta dauki matakin mayarwa da Jami’ar tsohon sunanta, bayan wani taro da gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranta a jiya Juma’a.

Idan ba a manta ba dai a watan Yulin shekarar 2017 ne tsohon gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya canjawa jami’ar suna zuwa Jami’ar Yusuf Maitama Sule, domin tunawa da marigayi Dan Masanin Kano Yusuf Maitama Sule, bisa irin gudummawar da ya bai’wa Jihar, dama Kasa baki daya.

 

Sai dai kuma a halin yanzu gwamnatin Jihar mai ci karkashin Jam’iyyar NNPP ta dauki matakin dawowa da Jami’ar tsohon sunanta.

Northwest University ya samo asali ne a zamanin mulkun tsohon gwamnan Jihar Dr Rabi’u Musa Kwankwaso ya samar da ita.

Continue Reading

Talla

Trending

%d bloggers like this: