Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tabbatarwa da ‘yan Najeriya cewar babu wanda zai iyayin kutse cikin na’urar tattara bayanai na hukumar domin sauya bayanan dake cikinta.

Babban mataimakin shugaban hukumar mai lura da sashen fasahar sadarwa Laurence Bayode ne ya tabbatar da hakan yayin zantawarsa da gidan talabijin na Channels.
Yana mai cewa babu wanda ya isa ya yiwa hukumar kutse ko sauya bayanai a ranar zabe.

Ya ci gaba da cewa yana da kwarin gwiwar tabbatarwa ‘yan Najeriya baza a iya yiwa na’urar kutse ba domin za su kiyaye gami da tabbatar da cewa ba’a yiwa na’urar kutse ba a ranar zabe.
