Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis ya bayyana cewa, ya gaya wa sabon Sarkin Birtaniya Sarki Charles Na Uku cewa shi bai mallaki gida a Tarayyar Turai ba.

Shugaba Buhari ya fadi hakan ne lokacin da yake amsa tambaya, a wani dan takaitaccen bidiyo da mai taimaka masa na musamman akan kafofin sadarwa Na zamani Tolu Ogunlosi ya wallafa a shafin Twitter.
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci sarkin a masarautar da ke Birtaniya.

Wannan shine karo Na farko Dai da Shugaba Buhari ya ziyarci Masarautar tun bayan darewar sabon sarkin kan karagar mulki. Sakamakon bai halarci taron nadin sarautar da akayi a baya ba.

Shugaba Buhari yace, lokacin da Sarki Charles Na uku ya tambaye shi ko ya mallaki gida a can Tarayyar Turai, sai yace masa a’a ko a Najeiya Gidajen da yake dasu ya Gina su ne tun kafin ya zama shugaban kasa.
Shugaban ya kara da cewa, bashi da burin mallakar kadarori a sassa daban-daban, yafi jin dadi idan yana zaune haka kawai kamar yadda yake ba tare da mallakar komai ba.