Shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya EFCC Abdurashid Bawa ya ce sauya fasalin kudi da za a yi a Najeriya zai karya darajar dalar amuruka zuwa naira 200.

Abduurrashin Bawa ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da sashen Hausa na gidan rediyo Jamus.
Ya ce dangane da sauya fasalin kudi da gwamnatin Najeriya za ta yi abu ne mai kyau kuma zai karya darajar dalar amuruka zuwa naira 200.

Tuni hukumar EFCC ta fara kamen masu sana’ar canjin kudi bisa zargin kawo cikas a ayyukan da gwamnatin ta sa a gaba.

Gwamnatin Najeriya ta kudiri aniyar sauya fasalin wasu kudi a kasar zuwa karshen watan Janirun shekarar 2023 mai zuwa.
Mutane da dama na kallon hakan ta fuska daban-daban tun bayan da shugaba Buhari ya bayyana karar cewar shi ya bayar da goyon baya domin sauya fasalin kudin.
Bankin Najeriya CBN ya bayyana cewar ya bi dukkan hanyoyi da su ka dace kafin sauya fasalin kudin kasar.
Allah yakarawa wannan mujalla daukaka Ameen