Hadakar rundunar ‘yan sanda da ‘yan sa-kai da Mafarauta a Jihar Neja sun hallaka wasu ‘yan ta’adda bakwai a Jihar.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Jihar Wasiu Abiodun shine ya tabbatar da faruwal lamari.

Abiodun ya ce lamarin ya farune a ranar Alhmis bayan kiran gaggawa da su ka samu daga al’ummomin kauyen Kumbashi da ke karamar hukumar Mariga ta Jihar.

Kakakin ya ce bayan zarya da ‘yan bindigan su ke yi a cikin kauyen ne ya sanya mazauna kauyen su ka kira jami’an tsaro.

Abiodun ya kara da cewa wasu daga cikin ‘yan bindigan sun tsere da raunuka a jikin su.

Kakakin ya kuma ce jami’an sa-kai biyu daga ciki sun samu raunuka inda aka mika ga Asibiti domin kula da lafiyar su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: