Anci gaba da sauraron shari’ar kisan Ummita, budurwar da ake zargi wani dan kaar China ya hallakata a Kano.

Bangaren gwamnatin jihar Kano karkashin kwamishinan Shari’a, Barista Musa Lawan Abdullahi, sun sake gabatar da shaidu a gaban Alkali.
Jaridar Daily trust ta ruwaito cewa a zaman ranar Jumu’a da ta gabata, an gabatar da Insifekta Injuptil Mbambu na sashen binciken aikata manyan laifuka ta hukumar yan sandan Kano a matsayin shaida na biyar.

Jami’in ɗan sandan ya faɗa wa babbar Kotun jiha cewa wanda ake zargi ya musu bayanin yadda ya haɗu da marigayya Ummukulsum wato Ummita har suka fara soyayya.

A cewar ɗan sandan, wanda ake zargi ɗan asalin kasar China, Mista Cheng, ya faɗa musu cewa Ummita ce ta fara karɓar lambarsa a hannun kawarsa mai suna Hanisa.
Daga nan ne su ka fara waya har suka kulla soyayya kuma ta masa alƙawarin zata aure shi a cewar mai ba da shaidar.
Bayan sauraron bayanan jami’in binciken,Alkalin Kotun mai shari’a Sanusi Ado Ma’aji, ya ɗage zaman zuwa watan ƙarshe shekarar 2022.
Ya ayyana ranakun 19, 20 da kuma 21 ga watan Disamban 2022 a matsayin ranar da za’a dawo domin ɗorawa daga inda aka tsaya.